Hukumar DSS ta kama masu fataucin yara a Kano

Hukumar, DSS, kama, fataucin, yara, Kano
Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) ta bankado wata kungiyar fataucin yara tare da kama wata mace ‘yar shekara 17 da gano wata yarinya ‘yar shekara 4 mai...

Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) ta bankado wata kungiyar fataucin yara tare da kama wata mace ‘yar shekara 17 da gano wata yarinya ‘yar shekara 4 mai suna Aisha da aka sace daga Nguru a jihar Yobe.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa ofishin Hukumar DSS na Kano, ya bayyana a ranar Talata cewa Jami’an Hisbah na Jihar Kano sun mika wata yarinya ‘yar shekara 4 mai suna A’isha da aka yi garkuwa da ita daga Nguru wacce wata mace ‘yar shekara 17 ta kawo Kano bayan sun yi garkuwa da ita, inda ake zargin cewa babu alaka tsakanin jaririn da aka sace da ita.

Karin labari: Kotu ta dage sauraren karar Rabi’u Kwankwaso da Hukumar EFCC

Hukumar DSS ta bayyana cewa bayan karbar Aisha ‘yar shekara 4 da aka sace tare da wanda ya sace ta, sun gano mutumin da ke safarar kananan yara daga Jihohin Makwafta inda aka sayar da su a Kudancin kasar nan.

Hukumar DSS ta ce bayan yiwa matar mai shekaru 17 tambayoyi, ta tabbatar musu da cewa mutumin da ta san yana sayar da goro ne ya rufe gidanta, ya shigar da ita cikin garkuwa ta hanyar cafke Aisha ‘yar shekara 4, kuma ya yi mata alkawarin cewa babu abin da zai same ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here