Rashin shigar da karar da Hukumar EFCC ta yi a gaban wata babbar kotun Kano ta hana ci gaba da sauraron karar da Dakta Rabiu Musa-Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP da wasu mutane bakwai suka shigar.
Acikin su akwai NNPP, Dakta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Clement Anele, Lady Folashade Aliu, Eng. Buba Galadima da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A lokacin da aka fara sauraren karar, Lauyan wanda ake kara, Mista Idris Ibrahim-Haruna, ya shaidawa kotun cewa bai shirya ba, ya kuma nemi a dage shari’ar domin a samu damar shigar da martanin nasu domin sauraren karar.
Karin labari: Majalisar Dattijan Najeriya ta amince kudirin mafi karancin albashin ma’aikata Naira 70,000
Da yake mayar da martani, Lauyan wadanda suka shigar da karar, Mista Robert Hon, ya shaidawa kotun cewa a shirye suke su ci gaba da sauraron karar.
Ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar wadanda ake kara na neman a dage shari’a saboda rashin baiwa kotun ainihin dalilin kin shigar da martani.
Ya bukaci kotun da ta dage ci gaba da sauraren karar.
Karin labari: Kotu ta kori karar da Iyalan Abacha suka shigar kan Gwamnatin Tarayya
Mai shari’a Yusuf Ubale ya umarci wadanda ake kara da su gabatar da amsarsu sannan ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, domin ci gaba da sauraren karar.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa a ranar 10 ga watan Yuni ne kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da hukumar EFCC kan cafke Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu mutane bakwai.