Ganduje ya taya Yusha’u murnar zamowa Dan arewa na farko a mukamin babban Edita a mujallar siyasa ta Afrika dake Harvard.

Dr. Muhammad Jameel Yushau 750x430 2
Dr. Muhammad Jameel Yushau 750x430 2

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya taya Dr Muhammad Jameel Yusha’u, dan asalin Kano murna, wanda ya karbi mukamin babban jami’in tantance ingancin labarai, edita a fitacciyar mujallar siyasa ta Africa, dake Havard.

Acikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Abba Anwar ya fitar a ranar Juma’a, ta ce kasancewarsa dan Arewa na farko da ya samu mukamin a Harvard, Gwamna Ganduje ya ce, “Muna alfahari da samun gwarzon malami matashi irinka da suka yi fice a fagen duniya.”

‘’ Ya ji dadi matuka kuma ya bayyana Yusha’u a matsayin ƙwararre wanda ya sauya harkar yada labarai da harkar sadarwa izuwa halin inganci datake ciki yanzu. Mun kuma samu labarin cewa ya taka rawa kwarai a lokacin da yake rike da mukamin babban jami’in kula da tsare-tsare na bankin ci gaban Musulunci, in ji sanarwar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Yusha’u, babban malami ne a fannin yada labarai da siyasa a jami’ar Northumbria da ke birnin Newcastle na kasar Birtaniya kuma malami a fannin aikin jarida na duniya na jami’ar Sheffield. Bayan ya bar Najeriya a matsayin malami a tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero dake Kano.

A cewar sanarwar, ya yi rubuce-rubuce da dama da ya daga darajar sa a mujallun nazarin kafofin watsa labarai da sadarwa na duniya, kamar su Global Media Studies, Journal of Arab and Muslim Media Research, da dai sauransu.

“Don haka a madadin gwamnatin Kano, ina taya Dakta Muhammad Jameel Yusha’u murnar samun wannan matsayi mai girma na Babban Editan Jaridar Siyasa ta Afrika da ya fito daga arewacin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here