Najeriya ta sake bude Iyakar Idiroko da karin wasu Iyakokin tsandauri guda 3

images 4
images 4

Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin da a bude Karin iyakokin kasar nan guda 4 da aka rufe su, tun watan Agustan shekarar 2019, domin dakile fasakaurin Shinkafa da nufin bunkasa harkokin Noman shinkafar da ake yi a Najeriya.

Ta cikin wata sanarwa da hukumar hana fasa kauri ta Najeriya ta fitar a ranar Juma’a, mai dauke da sa hannun mataimakin Kwanturola Janar na Kasa E. I. Edorhe, a madadin Kwanturola Janar Kanal Hameed Ali mai ritaya.

Sanarwar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin da a bude Iyakar Idiroko dake jihar Ogun, da Iyakar Jibiya dake jihar Katsina, da Iyakar Kamba dake jihar Kebbi, da kuma Ikom dake jihar Cross River.

Sanarwar mai taken ‘Sake bude karin iyakokin Najeriya guda 4’ tace “Biyo bayan umarnin farko da fadar shugaban Kasa ta bayar tun a ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2020, na a bude Kan iyakokin kasar nan na tsandauri guda 4 da suka hadar da; Mfum sa Seme da Illela da kuma Maigatari, an bani damar na sanar da ku cewa an bamu damar sake bude wasu karin kan iyakokin guda 4 kamar haka:

“Iyakar Idiroko dake Jihar Ogun (a shiyyar kudu maso yamma) sai Iyakar Jibia ta Jihar Katsina (a shiyyar Arewa maso yamma) sai Iyakar Kamba dake Jihar Kebbi (a shiyyar Arewa maso yamma) da kuma Iyakar Ikom dake Jihar Cross River (a shiyyar kudu maso Kudu)

A ranar 16 ga watan Decembar 2020 ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin farko, na a bude bodojin Mfum da Seme, da Illela da kuma Maigatari dake sassan kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here