An rufe daukacin makarantu a Sudan ta Kudu, sakamakon tsananin zafin da kasar ke fama da shi cikin makonni biyu.
Ma’aikatar lafiya da ilimi sun baiwa iyaye shawarar kar su bari ‘ƴa’ƴansu su fita, sakamakon hasashen tsananin zafin ka iya kai wa maki 45 a ma’aunin selshiyos.
Karin labari: An ƙayyade wuraren sayar da burodi da man fetur a Zamfara
Ma’aikatun sun ce, ana bibiyar yanayin sau da ƙafa, sai dai babu ranar buɗe makarantun.
Sun ce duk makarantar da aka samu a buɗe, za ta rasa lasisinta, kamar yadda hukumomin suka yi gargaɗi.
A makon da ya gabata ne, aka ba da rahoton mutuwar kimanin yara 15 sakamakon sanƙarau da wasu cututtukan da zafi ke haddasawa, in ji ma’aikatar lafiya ta ƙasar.