Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Juma’a, ta umurci tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da ya sauka daga kujerar sa ta ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓun Dass da Tafawa Balewa da Bogoro a jihar Bauchi.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Donatus Okorowo, ya bayyana cewa bayan sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, Yakubu Dogara bai cancanci ya ci gaba da zama kujerar ba saboda sashe na 68 (1) (g) na kundin tsarin mulki.
Mai shari’a Okorowo ya ƙara da cewa, hakan ya yi dai-dai da hujjar jam’iyyar PDP na cewa ta hanyar sauya sheka daga jam’iyyar da a doronta aka zaɓe shi zuwa majalisar dokoki ta tarayya kuma ya bar jam’iyyar kafin ƙarewar wa’adin sa, ya kama Dogara ya bar kujerar saboda bai cancanci shiga ayyukan jam’iyyar ba.
“Saboda haka kotun ta yi hukuncin ne don goyon bayan masu shigar da ƙara bisa da’awa da kuma bukatar su ta yin hukunci bisa adalci,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa jam’iyyar PDP da daya daga cikin mambobinta a jihar Bauchi su ne suka shigar da Dogara ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1060/20.
Sauran waɗanda ake ƙarar sun haɗa da ministan shari’a da hukumar zaɓe Mai zaman kanta INEC da kuma jam’iyyar APC.













































