Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta umurci dukkan jam’iyyun siyasar da ta yi wa rajista da su miƙa kwafin rajistar mambobinsu ga hukumar, domin bin sabuwar dokar zabe ta bana.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayar da umarni a taron ƙoli karo na biyu wanda hukumar ke gabatarwa duk wata uku na kwamishinonin zaɓe wanda ta gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce sabuwar dokar zaɗe ta wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa sunayen mambobinsu ga hukumar kwanaki 30 gabanin zaɓen fidda gwani.
“Bari kuma in yi amfani da wannan dama don tunatar da jam’iyyun siyasa cewa ta hanyar tanadin sashe na 77 na dokar zaɓe ta bana; Ana buƙatar kowace jam’iyya ta rike rijistar zama memba a jam’iyyar da ya haɗa da bugaggiyar takarda da kuma wanda ba a wallafa ba, sannan ta ba da irin wannan rajistar ga hukumar nan da kwanaki 30 kafin ranar da aka ƙayyade don gudanar da zaben fidda gwani da kuma babban taro.
“Ya zuwa yanzu, jam’iyyar siyasa ɗaya ce ta yi biyayya wajen miƙa bayanan duk da cewa wajibi ne dukkan su su gabatar.
“Yin wannan abu na rashin gabatar da bayanan kamar shiga zaɓe ne ba tare da rijistar masu zaɓe ba, Ba za a yi sahihin zaɓen fidda gwani ko kuma babban zaɓe na ƙasa ba tare da sahihin rijistar masu zabe ba,” inji Yakubu.
Shugaban na INEC ya kuma shawarci jami’an da su yi nazari sosai kan sabuwar dokar zaɓe, yana mai cewa ana kafa tsarin sahihin zaɓe ne a kan doka.
“Kamar yadda kuka sani, dokar zaɓe tare da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima da kuma ƙa’idojin gudanar da zaɓe, sun ƙunshi tsarin dokokin zaɓe.
“A matsayinmu na shugabannin hukumar zaɓe, ya zama wajibi a garemu mu san kanmu da tsarin doka.”
Dangane da ci gaba da rijistar masu kada kuri’a CVR da ake yi, musamman samar da ƙarin cibiyoyi don karkatar da aikin fiye da ofisoshin hukumar zaɓe ta ƙasa INEC a faɗin jihohi, Yakubu ya ce an samar da cibiyoyi 2,673.













































