Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansu Sanata Natasha Akpoti a Kogi

Natasha Akpoti 750x430

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansu Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta tsakiya, a Obeiba-Ihima, a karamar hukumar Okehi.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata, inda a kalla wasu mutane 3 dauke da bindigogi suka mamaye harabar gidan.

A cewar Yakubu Ovanja, babban jami’in tsaro na Sanatan, maharan sun isa wurin ne da misalin karfe 1 na safe inda suka lalata kadarorin, ciki har da farfasa tagogi.

Bayan kiran gaggawa da aka yi, jami’an tsaro daga Okehi sun kai dauki.

Karanta: Yan Najeriya miliyan 150 na da isasshiyar wutar lantarki – Minista

Ko da yake ba a kama wani mutum ba, amma an kididdige bayanan lamarin, kuma an fara gudanar da bincike na farko.

Da take rabbatar da harin Natasha ta ce mai yiwuwa maharan sun yi imanin cewa tana garin ne, lamarin da ya sa aka kai wa gidan danginta hari.

Ta kara da cewa babu wanda ya jikkata kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da Civil Defence sun fatattaki ‘yan bindigar.

TheCable

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here