Ministan wutar lantarki, Adedayo Adelabu, ya bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da karancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron ministoci na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin kokarin hadin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
A cewar Adelabu, Najeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 240, a halin yanzu tana samar da isasshen wutar lantarki ga mutane miliyan 150.
Karin karatu: Shettima ya gargadi shugaban hukumar NAHCON a kan yin aiki shi ɗaya tilo
Ministan ya bukaci masu hada-hadar kudi na duniya da su ba da fifiko wajen karfafa hanyoyin samar da wutar lantarki a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin wutar lantarki na Kaduna zai fara aiki kafin karshen shekarar 2025.
Dangane da kalubalen mitoci, Adelabu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa “ba da jimawa ba matsalar za ta zama tarihi.”
Da yake jawabi a kan tsarin hada-hadar kudi na bangaren, Adelabu ya bayyana cewa gyare-gyaren kudin wutar lantarki da aka aiwatar ya haifar da karuwar kudaden shiga na biliyan 700.
A watan Afrilun 2024, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da karin kudin fito ga abokan huldar kamfanin na Band A- wadanda ke samun wutar lantarki mafi karanci na sa’o’i 20 a kullum – daga ₦68 zuwa ₦225 a kowace kilowatt awa. Wannan karin kashi 230% ya shafi kusan masu amfani da wutar su miliyan 1.9.
A baya dai gwamnati ta bayyana cewa karin kudin ya zama dole saboda rashin dorewar tallafin makamashi, wanda aka yi hasashen za a kashe Naira tiriliyan 2.9 a shekarar 2024. Ko da aka yi karin kudin, har yanzu an kasafta Naira tiriliyan 2.8 don tallafin wutar lantarki a shekarar. NERC ta yi kiyasin cewa daidaita kudin harajin zai rage biyan tallafin da tiriliyan 1.14.