Hukumar tsarawa da cigaban Birane ta Kano (KNUPDA) ta rusa wani shago mallakar fitacciyar ‘yar TikTokel din nan Rahama Sa’idu da ke kan titin UDB a karamar hukumar Tarauni.
SolaceBase ta ruwaito cewa rugujewar wanda kuma ya shafi wasu gine-gine da dama, m Kwamitin kar ta kwana na KNUPDA ne ya gudanar da aikin a ranar Alhamis.
A cewar jami’ai, an yi gine-ginen ba bisa ka’ida ba a kan hanyoyin jama’a, wanda ya saba wa ka’idojin tsara birane.
Tun da farko dai shago Rahama Sa’idu ya shiga tsaka mai wuya a lokacin da KNUPDA ta cire alamar allon tallan shagon wanda ta sanya ba tare da izini ba.
Karin karatu: Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansu Sanata Natasha Akpoti a Kogi
Sai dai cire allunan ya sa Rahama Saidu ta kai rahoton lamarin ga hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Bayan korafin nata, shugaban hukumar ya gayyaci daraktocin KNUPDA da suka dace domin amsa tambayoyi game da lamarin.
Duk da haka, lamarin ya kara kaimi wajen aiwatar da aikin, kuma KNUPDA ta sake kaddamar da wani sabon rusau, inda ta nufi haramtattun gine-gine a yankin Tarauni, ciki har da bangaren shagon Rahma Saidu da aka gina a kan titin.
Jami’ai sun nanata cewa aikin wani bangare ne na kokarin maido da tsare-tsare na birane a Kano da kuma tabbatar da cewa ba a dakile hanyoyin zirga-zirgar jama’a da na tituna ta hanyar gine-gine ba tare da izini ba.