Hukumar NERC ta fara bincike kan kamfanonin rarraba wutar lantarki bayan ma’aikata 38 sun mutu a bakin aiki

NERC 5

Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa (NERC) ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan mutuwar ma’aikata 38 na wutar lantarki da suka rasu yayin aiki a cikin rukuni na biyu na shekarar 2025, inda duka mutanen suka fito daga kamfanonin rarraba wuta.

Rahoton na hukumar ya nuna cewa matakin kiyaye tsaro a harkar samar da wutar lantarki a Najeriya ya ƙara taɓarɓarewa a cikin wannan lokaci.

Hukumar ta ce adadin haɗurra ya karu daga 31 zuwa 60, yayin da mutuwa ta ƙaru daga 12 zuwa 38, sannan raunika suka tashi daga 14 zuwa 19 a cikin kwata ɗaya.

Hukumar ta bayyana cewa babu wani asarar rai da aka samu daga kamfanonin samar da wutar lantarki ko kuma kamfanin isar da ita, domin duk haɗurran sun faru ne a ɓangaren rarrabawa.

Daga cikin jimillar asarar da aka samu, kamfanonin Ibadan, Kano, Benin, Eko da Jos ne suka fi fuskantar matsala, inda suka tattara kashi 63 cikin 100 na dukkan haɗurran da aka ruwaito.

Hukumar ta nuna damuwa cewa kamfanonin rarraba wuta ne ke ci gaba da zama tushen haɗurra a masana’antar wutar lantarki, inda suka riƙa samun kaso mafi yawa na mutuwa tun shekarar 2024 har zuwa wannan shekara.

NERC ta bayyana cewa bisa tanadin sashi na 34(1)(e) na Dokar Wutar Lantarki ta 2023, tana da alhakin tabbatar da cewa ana samar da wuta cikin aminci da sahihanci ga jama’a.

Don haka, ta na karɓar rahotannin tsaro da lafiya daga kamfanonin wuta a kowane wata, kuma daga cikin rahotanni 105 da ake bukata, an samu 102 ne kawai a cikin wannan lokaci.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da tabbatar da cika kashi 100 cikin 100 na bayar da rahoton tsaro daga kamfanoni kamar yadda sharuddan lasisin su suka tanada, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa idan aka saba doka.

Duk da cewa kamfanin rarraba wuta (TCN) bai samu asarar rai ba, rahoton ya bayyana cewa an samu matsalolin lalacewar kayan aiki guda 11 saboda fashewa, gobara da ayyukan ɓarna.

NERC ta tabbatar da cewa ta riga ta kaddamar da bincike a kan dukkan waɗannan lamurra kuma za ta ɗauki matakan da suka dace bayan kammala bincike.

Haka kuma, hukumar ta ce tana aiwatar da tsare-tsare domin ƙarfafa al’adar kiyaye tsaro a tsakanin ma’aikatan masana’antar.

Hukumar ta kara da cewa tana sa ido sosai kan yadda kamfanoni ke aiwatar da dabarun rage haɗurra a fannin wutar lantarki, tare da shirya taruka kamar na manajoji masu kula da lafiya da tsaro domin inganta matakin tsaro a harkar samar da wutar lantarki ta ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here