Majalisar dokoki ta ƙasa ta buƙaci a gudanar da babban zaɓen ƙasa a watan Nuwambar 2026 maimakon a yi shi a 2027

national assembly 2

Majalisar dokoki ta ƙasa ta gabatar da shawarar a mayar da babban zaɓen a Najeriya zuwa watan Nuwamba shekara ta 2026, wato watanni shida kafin lokacin da aka saba gudanar da zaɓe a watan Fabrairu.

Shawarar na cikin kudirin dokar zaɓe mai suna Electrical act (wadda aka yi wa Gyara) ta 2025, wanda aka bayyana a ranar Litinin a wani taron sauraron ra’ayoyin jama’a da majalisar dattawa da majalisar wakilai suka shirya tare a Abuja.

Kudirin ya na da nufin a soke dokar zaɓe ta 2022, tare da kafa sabuwar doka mai ƙunshe da sauye-sauye da dama kan harkokin zaɓe.

A cikin wannan kudiri, an tanadi cewa zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni za su kasance aƙalla kwanaki 185 kafin karewar wa’adin mulkin masu rike da mukaman.

Wannan gyara na nufin tabbatar da cewa an kammala dukkan shari’o’in zaɓe kafin ranar rantsarwa ta 29 ga Mayu, 2027.

Masu tsara dokar sun ce matakin zai taimaka wajen hana jinkiri a shari’o’in kotu bayan zaɓe, amma sun nuna cewa ana bukatar a ƙarfafa tsarin shari’a domin ya iya shawo kan yawaitar ƙorafe-ƙorafen zaɓe.

Idan aka amince da wannan kudiri, hakan na nufin cewa zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni a Najeriya zai gudana ne a watan Nuwambar 2026, kusan watanni shida kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci.

Haka kuma, kudirin ya ƙunshi batutuwan kamar ba da damar yin zaɓe ga fursunoni, zaɓen ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje kafin lokaci, amfani da lambar shaida ta ƙasa wajen rajistar masu zaɓe, da kuma wajabta tura sakamakon zaɓe ta Internet.

Wani muhimmin sauyi kuma shi ne cewa amfani da katin zaɓe na dindindin (PVC) ba zai zama dole ba, domin tsarin BVAS baya karɓar bayanan da ke cikin na’ura ɗin katin.

Karin labari: Da ɗumi-ɗumi: Majalisar Koli ta amince da naɗa sabon shugaban hukumar INEC

Saboda haka, kowane mai zaɓe zai iya sauke katin nasa ta Internet kuma ya buga shi duk lokacin da bukata ta taso.

An bayyana cewa wannan mataki zai kawar da siye da sayar da katin zaɓe tare da tabbatar da tsarin tantance masu zaɓe ta hanyar dijital kaɗai.

Bugu da ƙari, an tanadi cewa duk jam’iyyun siyasa su kammala zaɓen fidda gwani da gabatar da sunayen ‘yan takararsu aƙalla kwanaki 210 kafin ranar zaɓe.

Har ila yau, sabuwar doka ta bai wa jam’iyyar siyasa damar kalubalantar tsarin zaɓen fidda gwanin wata jam’iyya ta daban, tare da takaita ikon kotu zuwa inda abin ya faru ko kuma babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

Majalisar dokoki ta kuma bayyana cewa tana shirin yin wani gyara a tsarin kundin tsarin mulki na 1999 domin ba da damar majalisa ta daidaita lokutan zaɓe ba tare da tsawaita tsarin gyaran kundin mulki ba.

Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai, sun tabbatar da cewa za a tabbatar da gaskiya da nuna adalci a duk matakan aikin.

Da zarar majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da kudirin, za a mika shi ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu domin ya sanya masa hannu.

Idan an amince, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa za ta sake tsara jadawalin zaɓe, wanda hakan zai sanya Najeriya ta gudanar da mafi gaggawar zaɓenta a tarihin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here