Hotuna: Rarara Ya Yi Hatsarin Mota

380607756 1888467754881048 1451843168405568340 n
380607756 1888467754881048 1451843168405568340 n

Fitaccen mawakin siyasa kuma shugaban kungiyar ’yan Kannywood na 13X13, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi hatsarin mota.

Mai magana da yawun mawakin, Rabiu Garba Gaya ne ya sanar a safiyar Juma’a cewa Rarara ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama, amma bai bayyana ko a ina ba ne.

380607756 1888467754881048 1451843168405568340 n 380639045 1888467658214391 5164815664537353540 n

A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, hadimin a Raraya ya dora hotunan yada motar mawakin ta fada a cikin wata katuwar lambatu da kuma yadda gaban motar ya yi kaca-kaca.

Sai dai ya bayyana cewa,  duk da hatsarin, Raraya yana cikin koshin lafiya.

(Aminiya)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here