Kotu ta yanke wa tsohon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau hukuncin ɗauri na shekara 35

317846298 10161007055477608 7586086777147872632 n
317846298 10161007055477608 7586086777147872632 n

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta yanke wa tsohon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba hukuncin ɗauri na shekara 35.

Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu, wadda ta yanke hukuncin ta ce an samu farfesa Garba ne da laifuka biyar da suka jiɓanci amfani da ƙarya wajen karɓar kuɗi da kuma zamba.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gaban kotu a ranar 12 ga watan Oktoba tana zargin sa da tatsar kuɗi daga wani mutum bisa alƙawarin ba shi kwangilar katange jami’ar, wadda kuɗinta ya kai naira biliyan uku.

A lokacin da ta yanke hukunci, mai shari’ar ta ce ta gamsu da bayanan da EFCC ta gabatar, sannan ta yanke masa hukuncin jimillar shekaru 35 a gidan gyaran hali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here