Zargin cin zarafi: An bada belin mawaki Seun Kuti

seun kuti 1 700x430 2
seun kuti 1 700x430 2

An saki shararren mawakin nan Seun Kuti daga hannun ‘yan sanda bayan ya cika sharuddan belinsa.

Lauyansa Adeyinka Olumide-Fusika (SAN) ya tabbatar da cewa an sake shi da misalin karfe 7:30 na yammacin Talata.

Fusika ya ce an saki mawakin bayan ya cika sharuddan belinsa.

Tawagar lauyoyin ta kuma tabbatar da cewa zai kasance a kotun majistare a ranar laraba domin cigaba da shari’ar. Manufar wannan shari’ar ita ce karbar shawarar Daraktan Hukumar Shari’a (DPP).

A ranar Talata babbar kotun ta majistare da ke zamanta a unguwar Yaba a Legas ba ta samu gudanar da zama ba.

Ba a bayar da wani dalili a hukumance na rashin halartar Alkalin Kotun Mai Shari’a Adeola Olatubosun da ta dade tana sauraren karar amma wata majiya ta shaida wa gidan Talabijin na Channels a waje cewa ta tafi halartar wani taro.

An kai Seun kotun majistare amma da aka samu labarin rashin zuwan alkalin, sai aka kai shi ofishin ‘yan sanda da ke Panti.

Daya daga cikin lauyoyin Seun Kuti ya ce an dage sauraron karar har zuwa yau, Laraba, 24 ga watan Mayu.

Lauyoyin nasa sun kuma ce sun bi ‘yan sanda zuwa Panti domin ganin yadda za su shirya sakin wanda suke karewa domin karin kwanaki hudu da kotu ta bayar a ranar Talata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here