Kungiyar CAJA ta bayyana tsarin da gwamnati za ta inganta rayuwar matasa a Kano

IMG 20230524 WA0055 750x430 1
IMG 20230524 WA0055 750x430 1

Wata kungiyar farar hula mai rajin tabbatar da shugabanci na gari da alkinta dukiyar al’umma wato  Center for Awareness on Justice and Accountability (CAJA) ta bayar da shawarar yadda ya kamata a aiwatar da sabbin tsare-tsare na manufofin ci gaban matasa a Kano domin magance tashe-tashen hankula da sauran matsalolin da matasa ke fuskanta a jihar.

Wakilin Jaridar SOLACEBASE ya ruwaito cewa babban daraktan cibiyar Kwamared Kabiru Saidu Dakata ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a lokacin da suka rattaba hannu kan kungiyar kare hakkin ci gaban matasa da gwamnatin jihar Kano.

Dakata wanda ya koka kan karuwar yawan al’ummar da ke da karancin kayan masarufi na rayuwa, inda suka damu da mummunan tasirin da lamarin ke yi a cikin al’umma.

Shugaban na CAJA ya koka gameda karuwar shaye-shayen miyagun kwayoyi, rashin aikin yi, sata da sauran munanan dabi’u da ke yaduwa a tsakanin matasa a jihar, ya kuma yi gargadin cewa irin wannan matsalar na iya haifar da babban kalubale, idan ba a dauki matakin gaggawa ba don dakile ta a lokacin da ya dace

Dakata ya bayyana cewa, sun yi hadin gwiwa tsakanin kungiyar CAJA da kungiyoyin matasan da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki tare da tallafi daga gidauniyar Youth Alive Foundation da USAID, inda suka bullo da tsare-tsare na musamman damin magance matsalolin musamman matasa a jihar.

Sai dai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta sanya hannu a kan takardar manufofin, kuma ta tabbatar da aiwatar da cikakken tsari da ayyukan samar da ci gaba mai dorewa ga bunkasar matasa da kuma hana tashe-tashen hankula.

Shugaban Youth Alive Foundation, Kingsley Ata ya ce gidauniyar tana cikakken haɗin gwiwa tare da CAJA da sauran masu ruwa da tsaki don haɓaka tsarin a cikin jihohi huɗu a matsayin shirin gwaji.

A nasa bangaren, kwamishinan matasa na jihar Kano mai barin gado, Kabiru Ado Lakwaya ya yaba da yunkurin na kungiyar CAJA da sauran masu ruwa da tsaki a kungiyar na ganin ta tallafa ga kokarin da gwamnati  ke yi akan lamarin tare da samar da tsari na ci gaban matasa.

Lakwaya wanda ya ya ba da tabbacin aiwatar da tsarin da za su magance manyan matsalolin matasa a Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here