Gwamnatin Kano ta amince da biyan alawus na tsawon watanni 11 ga masu gadin gandun daji

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da biyan albashin watanni 11 ga masu gadin gandun daji 100.

Majiyar SolaceBase ta ruwaito cewa majalisar a zaman da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a ranar Litinin din da ta gabata ta bada izinin biyan albashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ya kai Naira 11,000,000.00.

Hakazalika, majalisar zartaswar jihar ta amince da sake duba kashi 100 cikin 100 na alawus alawus na masu gadin gandun daji a karkashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi a duk wata.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a ranar Talata, majalisar ta amince da ware kudi Naira 265,803,510.00 ga ma’aikatar kasa da tsare-tsare domin biyan diyya ga masu kadarori, da fadada jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil ya shafa.

Haka kuma ma’aikatar an ba ta Naira 81,142,850.00 domin biyan diyya da ya shafi ginin titin Panda – Hamdullahi – Albasu – Sakwayen Dutse.

Karin karatu: Ranar Ma’aikata: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu

Har ila yau, an amince da kashe Naira3,469,629,136.81 ga ma’aikatar ayyuka don samar da fitilu masu amfani da hasken rana a fadin birnin Kano a karkashin shirin sabunta birane.

Ya ce an ba da izinin kashe Naira 185,162,487.50 ga ma’aikatar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire.

Majalisar ta amince da Naira 327,780,226.89 ga ma’aikatar ilimi domin biyan wasu basukan da ake bin fannin ilimi.

An baiwa ofishin sakataren gwamnatin jiha Naira 240,506,500.00 domin siyan motocin kashe gobara don amfani da su a gidan gwamnati.

An amince da Naira 390,361,730.83 ga ma’aikatar ayyuka don samarwa da kafa na’urorin hawa a Gidan Murtala da Gidan Ado Bayero.

An amince da Naira 122,161,145.87 ga wannan ma’aikatar don ayyukan gyare-gyare a sashin albarkatun ilimi na Kano (KERD).

An kuma amince da kashe Naira 409,444,909.13 domin gudanar da ayyukan gyara gaba daya gidan Gwamnan Jihar Kano, dake titin Sultan, Kaduna.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta soke shirin tallafin karatu na kasashen waje

Don ci gaba da inganta ayyukan more rayuwa, majalisar ta amince da kashe Naira 105,403,453.62 ga ma’aikatar ayyuka don gina titin Miller zuwa titin manufa.

An warewa ma’aikatar ilimi Naira 1,212,571,013.79 domin inganta makarantar koyon addinin musulunci (SIS), a kananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Ungogo.

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta samu amincewar Naira 1,698,800,000.00 domin biyan kudin wutan lantarki, dizal da man fetur na watannin Janairu zuwa Maris 2025 a hedikwatar Hukumar Ayyuka da Ruwa ta Kano.

Daga cikin wasu sanannun ayyuka da aka yarda a yi su:

Za a kashe Naira 115,959,502.88 domin aikin gyaran masallacin Juma’a da ke garin Amana;

Sai Naira 303,399,484.20 domin gina masallacin Juma’a da taimakon ayyukan raya kasa a Rijiyar Gwangwan, karamar hukumar Dawakin Kudu;

Sai kuma Naira 274,770,887.84 domin gina katangar a gidan gwamnatin jihar Kano;

Za a kashe Naira 1,468,685,912.17 don gyarawa da inganta ma’aikatar wutar lantarki da sabunta makamashi a Sharada Phase I;

Yayin da za a kashe Naira 5,492,077,139.05 domin gyaran hanyoyin da suka taso daga Gidan Mallam Aminu Kano (Gidan Mumbayya) zuwa shatale-talen Tal’udu, Gadon Kaya, titin Yahaya Gusau da Sharada;

Sai kuma Naira 15,667,634,645.10 ga ‘yan majalisa da kuma alawus-alawus na tsofaffin kansilolin da suka yi aiki tsakanin 2014 zuwa 2024;

Sannan za a kashe Naira 5,386,380,955.00 don ci gaba da shirin tallafin karatu na kasashen waje da fara shirin tallafin karatu na gida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here