Wata gobara da ta tashi da daddare a Jos, babban birnin jihar Filato, ta lalata wasu sassa na shahararriyar kasuwar Terminus da ke Jos.
Kayayyaki da kadarori na miliyoyin nairori sun kone a gobarar, wanda tun daga lokacin aka fara shawo kan gobarar, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Karin karatu: Gwamnatin Kano ta amince da biyan alawus na tsawon watanni 11 ga masu gadin gandun daji
Wani shaidar gani da ido ya ce gobarar ta tashi ne ‘yan mintoci bayan karfe 11 na daren ranar Talata, inda ta yi barna da shaguna da dama da kayayyaki da dama.
Kawo yanzu dai hukumomi ba su tantance ainihin musabbabin tashin gobarar ba.













































