Naira miliyan 300: Gwamnatin Rivers ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan NBA

NBA Rivers Administrator 750x430

Gwamnatin jihar Rivers ta yi gargadi ga kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), inda ta bukaci a mayar musu da kudaden da ake ta cece-ku-ce a kan su na Naira miliyan 300 miliyan da ta biya a matsayin “tallafin karbar baki” na babban taron shekara-shekara na 2025, inda ta yi barazanar daukar matakin shari’a idan ba a dawo mata da su ba.

Gargadin ya biyo bayan matakin da NBA ta dauka na mayar da babban taron ta na 2025 daga Fatakwal jihar Rivers zuwa jihar Enugu, matakin da gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin cin amana.

A wata sanarwa da Hector Igbikiowubo, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Admiral Ibok-Etteh Ibas (mai ritaya), gwamnatin jihar Ribas ta yi watsi da ikirarin NBA na cewa Naira miliyan 300 “kyauta” ce kuma ba ta da alaka da karbar bakuncin AGC.

A cewar gwamnatin, an yi yarjejeniyar ne bisa gaskiya, tare da fatan gudanar da babban taron wanda zai kawo wa jihar da al’ummarta gagarumin fa’idar tattalin arziki.

Gwamnati ta soki shawarar da NBA ta yanke na mayar da taron a matsayin “rashin da’a,”.

Gwamnatin ta kuma yi gargadin cewa idan hukumar NBA ta kasa mayar da kudaden, za ta bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin kwato kudaden, wadanda ta bayyana a matsayin “dukiyar mutanen jihar Rivers.”

Duk da wannan cece-ku-ce, gwamnatin jihar Rivers ta sake jaddada shirinta na yin hadin gwiwa da kwararrun hukumomi, ciki har da hukumar NBA, amma ta yi gargadin cewa “ba za ta dauki nauyin cin zarafin jama’a da gwamnatin jihar Ribers ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here