Kwamitin wucin gadi da zai sanya ido a jihar Rivers, ya gayyaci shugaban rikon jihar Rivers Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) da ya gurfana a gabanta a ranar Alhamis don tattaunawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi (Jnr), ya fitar a ranar Laraba.
Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin mai mambobi 21 karkashin jagorancin Farfesa Julius Ihonvbere wanda kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya kaddamar a ranar Talata.
Majalisar dai ta kafa kwamitin ne biyo bayan kudurin da majalisar dokokin kasar ta yanke na amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers.
Karin karatu: Naira miliyan 300: Gwamnatin Rivers ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan NBA
Rotimi a cikin sanarwar ya ce kwamitin ya bayar da gayyatar ne a taron farko na ranar Laraba, biyo bayan kaddamar da kwamitin da shugaban majalisar, Abbas Tajudeen ya yi a ranar Talata, 15 ga Afrilu, 2025.
Ya ce gayyatar za ta samar da wani tsani ga mambobin majalisar domin tattaunawa kan rahotannin farko da kuma abubuwan da ke fitowa daga jihar Rivers tun lokacin da aka naɗa shugaban jihar shi kadai.
Ana sa ran shugaban ya gurfana gaban kwamitin a ranar Alhamis, 17 ga Afrilu, 2025, da karfe 4:00 na yamma, a daki mai lamba 414, Sabon Ginin Majalisar Wakilai, Rukunin Majalisar Tarayya a Abuja.