Fadar White House ta hana kamfanin dillancin labarai na AP da Reuters daukar rahoton taron majalisar ministoci

Trump 1

Fadar White House ta hana ‘yan jaridu daga kamfanin dillancin labarai na Reuters da sauran kafofin yada labarai damar shiga taron majalisar ministocin shugaba Donald Trump na farko da ya dace da sabbin manufofin gwamnatin dangane da yada labarai.

Fadar White House ta ki bada damar ganawa da wani mai daukar hoto na Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press da kuma ‘yan jarida uku daga Reuters, HuffPost da Der Tagesspiegel, wata jaridar Jamus.

Ma’aikatan gidan Talabijin daga ABC da Newsmax, tare da wakilai daga Axios, Blaze, Bloomberg News da NPR an ba su izinin shiga wajen taron.

Tun da farko dai gwamnatin Trump ta sanar da cewa fadar White House za ta tantance kafafen yada labaran da za su rika yada labaran shugaban a kananan wurare kamar ofishin Oval.

Karanta: Amurka ta musanta batun tallafawa ayyukan Boko Haram ta hannun USAID – Jakada

Kungiyar masu aiko da rahotanni ta fadar White House a al’adance ta tsara yadda za’a gudanar da taron manema labarai na shugaban kasaz inda Reuters ta kasance tana gudanar da ayyukan ta tsawon shekaru.

Sakatariyar yada labaran fadar White House Karoline Leavitt ta ce yayin da za a ci gaba sa bai wa tsoffin kafofin yada labaraidamar yada labarai na yau da kullun na Trump, gwamnatin na shirin sauya wadanda ke shiga cikin wannan wuri. (Reuters/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here