Gwamnan Kano ya ba da umarnin yin bincike kan batun zaftare albashin ma’aikata

Abba Yusuf Kano Governor1

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka kan yadda rahotannin ke yaduwa na rashin biyan albashin ma’aikatan jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin ma’aikata da kuma cin amanar jama’a.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis.

Da yake tona asirin yadda wasu ma’aikatan suka kwashe watanni ba tare da samun kudaden da suka dace ba, Gwamna Yusuf ya sha alwashin fallasa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Haka kuma, gwamnan ya kaddamar da wani kwamitin bincike mai cikakken iko domin gano musabbabin wannan batu, walau sakamakon kuskure na fasaha ko kuma da gangan don yin zagon kasa.

Karin albashi: Haɗarin Aiki: Ma’aikatan NAFDAC sun bukaci a kara musu albashi

SolaceBase ta bayar da rahoton cewa an umurci kwamitin da ya gudanar da cikakken bincike na albashin jihar daga watan Oktoban 2024 zuwa Fabrairun 2025, don gano ma’aikatan da abin ya shafa, da tantance su tare da ba da shawarar gyara da ladabtarwa.

Kwamitin mai mutane bakwai, karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, Kwamishinan Karkara da ci gaban Al’umma kuma tsohon Akanta Janar na Jiha, ya kunshi manyan jami’an gwamnati da masana harkokin kudi masu zurfin sanin tsarin biyan albashi.

Membobin kwamitin sun hada da:

1. Hon. Abdulkadir Abdussalam – Shugaba

Kwamishinan Ma’aikatar Karkara da ci gaban Al’umma

2. Dr. Bashir Abdu Muzakkari – Mamba

Mashawarci na Musamman akan Tattalin Arziki na zamani

3. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Mamba

Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano

4. Dr. Hamisu Sadi Ali – Mamba

Darakta Janar na ofishin kula da basussuka na jihar Kano

5. Hajiya Zainab Abdulkadir – Mamba

Daraktan Cibiyar koyar da na’ura mai ƙwaƙwalwa ta Jihar Kano

6. Aliyu Muhammad Sani – Sakatare

Darakta, Bincike a Ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano

7. Ummulkulthum Ladan Kailani – Babban Sakatare

Babban Mataimakin Sakatare (AGS), mulki da gudanarwa na ma’aikata a ofishin sakataren Gwamnatin jihar Kano.

Karanta: Gwamnatin Kano ta amince da biyan bashin albashin watanni tara ga ma’aikatan tsafta 2,369

Gwamnan ya ba wa kwamitin kwanaki bakwai kacal ya kammala bincikensa tare da gabatar da cikakken rahoto da ke bayyana wadanda ke da hannu a cikin lamarin, da irin tabarbarewar harkokin kudi, da kuma mafita mai dorewa don tabbatar da cewa matsalar ba ta sake faruwa ba.

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa da ma’aikatan gwamnati cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da kuma biyan albashi cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin cin zarafin ma’aikata zai fuskanci mummunan sakamako.

A daidai lokacin da kwamitin ya fara aiki, ana sa ran cewa, wannan yunkuri zai bankado yadda ake tafka magudi a cikin albashi, da maido da kwarin gwiwa kan tsarin albashin jihar, da kuma kare hakkin ma’aikatan jihar Kano masu fafutuka.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here