Gwamnatin Kano ta amince da biyan bashin albashin watanni tara ga ma’aikatan tsafta 2,369

Abba Yusuf Kano Governor1

Majalisar zartaswar jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da biyan bashin albashin watanni tara ga ma’aikatan tsaftar muhalli 2,369 a fadin jihar.

Biyan dai ya kunshi wasu kudade daga watan Yunin 2024 zuwa Fabrairu 2025 kuma Majalisar zartaswa ta Jihar Kano ce ta dauki nauyin biyan.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce amincewar wani muhimmin mataki ne na tallafawa dorewar muhalli a jihar.

Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar ‘yan kasarta da kuma tsaftar muhalli.

Karin labari: Tsaftar muhalli: Za mu hukunta masu karya dokokin tsaftar muhalli da kuma fito da sabbin tsare-tsare

“Ma’aikatan tsaftar muhalli wadanda suka taka rawa wajen tabbatar da tsafta a fadin jihar Kano, sun nuna hakuri a watannin da suka gabata yayin da suke jiran a biya su dbashi.”

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Dr. Hashim ya kuma nuna jin dadinsa ga majalisar zartarwa ta jihar Kano bisa tallafin da ta bayar wajen saukaka biyan kudaden.

Bugu da kari, Kwamishinan ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a tantance sauran ma’aikatan tsaftar muhalli da suka hada da ƴan duba gari, da ‘yan kungiyar tsaftar muhalli ta Vanguard don samun irin wannan damar.

Ma’aikatar tana kira ga wadannan ma’aikata da su kasance cikin shiri don tantancewa da biyan kuɗin na su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here