Majalisar dattijai ta gayyaci mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu domin ya yi bayani kan kudaden da ake zargin hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) na tallafa wa kungiyar Boko Haram.
Haka kuma an gayyato shugabannin hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da da hukumar tsaro ta sirri (DIA) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
A cewar babban zauren majalisar, ganawar da shugabannin wadannan hukumomin tsaro za ta kasance a cikin sirri.
Kudurin gayyatar su ya biyo bayan kudirin da Sanata Ali Ndume na jam’iyyar APC daga jihar Borno ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba a Abuja.
Karin karatu: Ribadu ya miƙa wa gwamnatin Kaduna mutane 59 da aka ceto daga masu garkuwa da su
An gabatar da kudirin ne sakamakon wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta inda dan majalisar dokokin Amurka Scott Perry ya yi ikirarin cewa hukumar ba da agaji ta Amurka, USAID, ta tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Ndume ya kara da cewa, a tsawon shekarun da suka gabata, gwamnatin tarayya ta yi kokari matuka wajen aiwatar da matakan dakile ayyukan kungiyoyin ta’addanci, tare da kashe makudan kudade.
Sai dai ga dukkan alamu wadannan yunƙurin sun haifar da taƙaitaccen sakamako, saboda ayyukan ta’addancin sun ci gaba da wanzuwa.
Ya ce babban barnar da ‘yan Boko Haram ke yi a Najeriya ya kamata ya zama abin damuwa domin ya zubar da kimar kasar a tsakanin al’ummomi.
Ndume ya ce tun a wannan lokaci ne aka fara zargin cewa wasu kungiyoyin kasa da kasa ne ke da hannu wajen aikata munanan ayyukan.
Don haka ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa domin tona asirin.
Sanata Shehu Kaka (APC-Borno), wanda ya goyi bayan kudurin ya ce zargin yana da nauyi, yana mai cewa ‘yan fashi da sauran laifuka sun shafi kananan hukumomin 109 na majalisar dattawa.
Sanata Abdul Ningi na jam’iyyar PDP daga jihayBauchi ya ce ba zai yiyu ba majalisar dattawa ta iya tuntubar majalisar yadda ya kamata ba tare da shigar da jami’an tsaro da abin ya shafa ba, wadanda ya kamata a gayyace su su yi wa majalisar bayani kan lamarin.
Don haka Ningi ya bukaci majalisar dattijai da ta gabatar da kudiri guda na gayyatar hukumar NSA, da kuma shugabannin hukumar DSS, NIA, da DIA, domin yiwa majalisar bayani kan wannan zargi.
A nasa jawabin, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya godewa Ningi bisa gudunmawar da ya bayar, ya kuma jaddada cewa ya kamata hukumomin tsaro da abin ya shafa su yiwa majalisar bayani a wani zaman sirri da za a yi.
Ya kuma lura cewa bai kamata a rika tattaunawa da irin wadannan batutuwan tsaro a bainar jama’a ba.(NAN)