Tinubu yayi sabon naɗi

tinubu 2

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Dakta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin fasahar jiragen sama na kasa NCAT da ke Zariya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana cewa, Dakta Ismaila kwararre ne a fannin kula da harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki da sufuri, da tsaron jiragen sama, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin “Physics” a shekarar 1989.

Karanta: Gwamnatin tarayya za ta binciki harin jirgin sama da ya kashe mutum 10 a Sokoto – Ministan Tsaro

Ya kuma yi Difloma a fannin Sufuri kuma ya halarci kwasa-kwasai da yawa, da karawa juna sani kan kula da zirga-zirgar jiragen sama.

Kafin nadin Dr Ismaila malami ne a jami’ar sufuri ta tarayya dake Daura.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here