A Gaggauce: NNPP ta kori shugaban jam’iyyar na Kano, Dungurawa makonni biyu bayan sake zaɓensa

dungurawa

Shugabannin zartarwa na jam’iyyar NNPP a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano sun kora tare da fitar da shugaban jam’iyyar na jiha, Hashimu Dungurawa, daga jam’iyyar.

Jimillar shugabanni zartarwa 27 ne suka sanya hannu kan kudurin amincewa da matakin, wanda aka cimma a taron zartarwa na biyu na mazabar, makonni biyu bayan babban zaɓe, ƙarƙashin jagorancin shugaban mazabar, Shuaibu Hassan, tare da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa.

A cewar kudurin, an dauki matakin ne bisa zarge-zargen haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyya, tayar da rikice-rikicen cikin gida, kasa biyan kuɗaɗen jam’iyya, da kuma yin kalaman cin mutunci ga gwamnan jihar Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugabannin mazabar sun bayyana cewa halayen da ake zarginsa da su ba za a amince da su ba, kuma suna cutar da martaba, haɗin kai da ci gaban jam’iyyar NNPP.

Karin labari: Shirin Gwamnan Kano na ficewa daga NNPP zuwa APC

Sun jaddada cewa an dauki matakin ne bisa bin kundin tsarin jam’iyyar, tare da nuna muhimmancin kiyaye ɗa’a, haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.

Shugabancin mazabar ya bayyana cewa an tura kwafen kudurin zuwa ofisoshin jam’iyyar na ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa domin ɗaukar matakan da suka dace, tare da sanar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Sun kuma jaddada cikakken biyayya ga shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa ƙarƙashin Sanata Kwankwaso, tare da alkawarin ci gaba da goyon bayan gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, suna mai cewa wannan mataki zai zama darasi ga duk wanda ke tauye dokoki da ɗa’ar jam’iyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here