Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar fashewar wani abu mai ƙara da sanyin safiyar Talataba babban asibitin Bagudo da ke ƙaramar hukumar Bagudo a jihar.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi, wadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya samu.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu cikakken iko da halin tsaro a yankin bayan jin ƙarar fashewar da ta auku a babban asibitin na Bagudo da safiyar ranar.
Sanarwar ta bayyana cewa wata ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa da ta haɗa da ƴan sanda, sojoji da jami’an tsaron sa-kai ta killace tare da tabbatar da tsaron yankin da abin ya shafa cikin gaggawa, yayin da ƙwararrun jami’an cire abubuwan fashewa da masu binciken sinadarai suka fara tantancewa a wurin.
Rahoton ya nuna cewa babu asarar rai sakamakon fashewar, duk da cewa wani gini a gidajen ma’aikata ya lalace, inda mazauna wurin suka riga suka ficewa cikin aminci kafin abin ya faru.
A cewar sanarwar, kwamishinan ƴan sandan jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kare doka da oda.
Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa bincike mai zurfi na gudana domin gano musabbabin fashewar, tare da kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma guji kusantar yankin har sai an kammala ayyukan tsaro da bincike.













































