Gwamnatin Zamfara ta nemi afuwar kan rufe gidajen rediyon NTA da tashar tarayya ta Pride FM Gusau da wasu Hukumomin yada labarai masu zaman kansu guda uku.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa sauran gidajen yada labarai da gwamnatin ta rufe sun hada da Gamji TV da Gamji FM da kuma Al-umma TV.
Gwamnatin, a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar, ta yi zargin cewa kafafen yada labaran da abin ya shafa sun karya dokar zartarwa mai lamba 10 tare da cin zarafin aikin jarida.
Dokta Abdullahi Shinkafi, jigo a jam’iyyar APC kuma shugaban kwamitin shari’ar ‘yan fashi da laifuka na jihar Zamfara, ya mika neman afuwar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.
Shinkafi ya ce gwamnati ta fusata ne bisa zargin karya dokar zartarwa mai lamba 10, 2022, wacce ta fara aiki a ranar 13 ga Oktoba.
A cikin wannan oda, gwamnati ta haramta duk wani gangamin siyasa da tarukan siyasa a jihar saboda matsalar tsaro, tare da dakatar da duk wasu shirye shiryen siyasa a jihar tare da rufe hanyoyin a kananan hukumomin Anka, Bukuyum da Gummi baki daya da sauran garuruwa da kauyukan da abin ya shafa.
Shinkafi ya ce kungiyoyin kafafen yada labaran da abin ya shafa sun karya dokar ne ta hanyar halattar gangamin taron siyasa na dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Dr Dauda Lawal-Dare a Gusau ranar Asabar.
Hukumar kulada kafafe labarai ta Najeriya NBC, kungiyar yada labarai ta Najeriya BON, kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ da dai sauransu, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, tare da yin kira da a gaggauta sake bude su.













































