Hukuncin Kotun Koli: Hisbah Za Ta Ci Gaba Da Rufe Shagunan Yin caca a Kano

hisbah officials

Hukumar Hisba ta Kano za ta ci gaba da yaki da shagunan caca bayan wata kotu koli ta yanke hukunci kan hana caca.

SolaceBase ta rahoto cewa Kotun Koli ta yi watsi da wata doka ta 2005 ranar Juma’a wadda ta hallarta yin caca.

Kotun ta yanke hukuncin cewa tsarin caca lamari ne na gwamnatocin jihohi.

Jihar Kano dai na daya daga cikin jahohi 12 mafi yawan musulmin Najeriya da ake amfani da shari’ar musulunci a cikinsu tare da dokar tarayya.

“Za mu dawo da murkushe shagunan caca tare da sabunta kuduri tunda yin caca ya sabawa doka a karkashin dokar shari’ar jihar Kano,” Abba Sufi, daraktan hukumar Hisbah ta Kano, ya shaidawa AFP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here