Shugaba Tinubu ya sahale kudirin gyaran rancen kudi ga dalibai

Tinubu, najeriya, sahale, kudiri, rance, kudi, gyaran, dalibai, najeriya
Shugaban Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin gyaran rancen dalibai na kasa ya zama doka, kamar yadda NTA ta rawaito a ranar Laraba. SolaceBase ta...

Shugaban Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin gyaran rancen dalibai na kasa ya zama doka, kamar yadda NTA ta rawaito a ranar Laraba.

SolaceBase ta rawaito cewa Tinubu ya rattaba hannu kan dokar rancen ɗalibai ta zama doka a watan Yuni 2023 don ba da tallafin kuɗi ga ɗaliban Najeriya a manyan makarantu.

Karin labari: Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin wutar lantarki

Sai dai an jinkirta aiwatar da dokar saboda wasu batutuwa da ke kawo cikas wajen fitar da ita.

An yi wasu manyan gyare-gyare a kan dokar tare da sake yin aiki kafin Tinubu ya sanya hannu.

Karin labari: Kungiyar NCAC ta shawarci shugaba Tinubu kan mayar da Betta Edu matsayinta

Dokar dai na da nufin baiwa asusun baiwa ’yan Najeriya da suka cancanta rancen kudi da kuma kula da su a lokacin karatunsu a manyan makarantun da aka amince da su da cibiyoyin koyon sana’o’i a Najeriya da sauransu.

Cikakken labarin na nan tafe…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here