Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Gombe, Alhaji Jamil Gwamna, a ranar Talata, ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar.
A cikin wasikar murabus din da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazabar sa Jekadafari, Gwamna ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne bayan tattaunawa da iyalansa da abokan siyasa da kuma magoya bayansa.
An mika kwafin wasikar mai kwanan wata 1 ga Fabrairu, 2022 ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ranar Talata a Gombe.
Wasikar nq cewa: “Na rubuto cikin tawali’u da mutuntawa, domin in sanar da ku shawarar da na yi na ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki.
“Na dauki matakin ne bayan tattaunawa da dangi, abokan siyasa, da magoya bayana. Na yaba da irin goyon baya da gata da nake samu a jam’iyyar. Ina yiwa jam’iyyar fatan alheri; Na gode.”
NAN ta ruwaito cewa Kafin zaben gwamna na 2019, Alhaji Jamil Gwamna, ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP.













































