Wata ‘yar jarida mai shekaru 26 ta lashe kujerar majalisa a jihar Kwara

IMG 20230319 WA0019
IMG 20230319 WA0019

Wata ‘yar jarida mai shekaru 26, Rukayat Motunrayo Shittu, ‘yar takarar jam’iyyar APC a zaben mazabar Owode/Onire a karamar hukumar Asa ta lashe zaben majalisar dokokin jihar.

Zaben wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

An tattaro cewa ‘yar takarar APC ta samu kuri’u 7,521 inda ta doke abokin takararta a jam’iyyar PDP, wadda ta samu kuri’u 6,957 a zaben na ranar Asabar.

Hakan ya sanya ta zama daya daga cikin ‘yan takara mafi karancin shekaru a Najeriya da suka yi takara tare da lashe kujerar siyasa.

Da take jawabi bayan an bayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara, Rukayat ta ce ta ji dadi matuka, bisa bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben a mazabar Owode Onire, kuma ta yaba wa jam’iyyarta, shugabannin jam’iyyar, da masu kada kuri’a da suka ba ta abin da ta bayyana a matsayin wata dama ta baya.

“Ana mayar da matasa da mata saniyar ware a siyasar Najeriya amma Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq ya gyaran fuska kan wannan tirka tirkar a Kwara.

Zan tabbatar na inganta tare da karfafa gwiwar matasa da mata su shiga harkar siyasa,” inji ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here