Rahoton shekara-shekara kan tsaro a jihar Kaduna, wanda ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar ta gabatar, ya ce akalla mutane 1,192 ne ‘yan ta’adda suka kashe a shekarar 2021.
Haka zalika, an yi garkuwa da mutane 3,348, yayin da a kalla mutane 891 suka samu raunuka sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da wasu munanan hare-hare a lokaci guda.
Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, ya gabatar da rahoton ga Gwamna Nasir El-Rufa’i da sauran jami’an gwamnati, a ranar Talata, a Kaduna a zauren Majalisar Zartarwa na Gidan Gwamnati.
Rahoton da aka yi bitar ya ce an sace shanu 13,788 a fadin jihar cikin watanni 12.
A cewar rahoton jihar ta samu asarar gonaki 182 ko dai ta hanyar shanu, a karkashin kulawar makiyaya, ko kuma makiyayan da ‘yan bindiga suka sace wadanda suka lalata gonaki yayin tserewa.
Ta ce barnar ta bayyana sosai a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun, Kajuru, Jema’a, Kaura, Kauru da Zangon Kataf.
Rahoton ya nuna cewa yara 50 na daga cikin wadanda aka kashe, yayin da 1,038 maza ne, 104 kuma mata ne.
A Kaduna ta tsakiya ne aka fi samun adadin wadanda suka mutu ya kai 720, sai 406 a Kaduna ta Kudu sai 66 a Kaduna ta Arewa.
Rahoton ya ci gaba da cewa an sace shanu 10,261 a shiyyar Kaduna ta tsakiya, 1,941 da kuma 1,586 an sace su a shiyyar Kudu maso Kudu da Arewa.













































