Easter: A kawo karshen wahala da rashin tsaro a Najeriya – Kukah ya bukaci Tinubu

speaker bishop kukah

Bishop Matthew Kukah na cocin Katolika a jihar Sokoto ya fitar da sakon Easter mai zafi ga shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya bukace shi da ya kubutar da ‘yan Najeriya daga abin da ya bayyana a matsayin “tsananin wahala, rashin tausayi, da rashin makoma.

Da yake jawabi a yayin bikin Easter a ranar Asabar, Kukah ya kwatanta wahalar da ‘yan Najeriya ke sha da giciyen Kristi, da nuna alhinin rashin tsaro, yunwa, fatara, da gurbacewar tarbiyya a fadin kasar nan.

A yayin da yake tabbatar da cewa Tinubu bai haifar da da dama daga cikin matsalolin da suka addabi al’umma a halin yanzu ba, Kukah ya jaddada cewa a yanzu alhakinsa ne ya jagoranci kasar nan wajen samun waraka da dawo da martabarta.

Kukah ya soki yadda rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa, inda ya yi tsokaci kan karuwar sace-sacen jama’a da yadda tashe-tashen hankula suka yi kamari a tsakanin al’umma, da kuma matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ke kara ta’azzara sakamakon kawar da tallafi da hauhawar farashin kayayyaki.

“Ya Shugaba, don Allah ka saukar da mu daga wannan raɗaɗi na yunwa,” in ji shi yayin da yake kira ga gwamnati da ta mayar da abinci a matsayin ‘yancin ɗan adam kuma abu mai saukin samu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here