IGP ya gargadi rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

IGP, Kayode Adeolu Egbetokun, 'yan sanda, najeriya, gargadi, runduna
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’i na karbar kudi tare da yin gargadi ga duk wani...

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’i na karbar kudi tare da yin gargadi ga duk wani jami’in da ya yi amfani da su ko amfani da sunansa wajen aikata miyagun ayyuka.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Sufeto Janar din ya nuna matukar damuwarsa, inda ya jaddada cewa irin wannan aika-aikar na zubar da mutuncin sa da kuma rundunar ‘yan sanda, wanda hakan ke zubar da mutuncin jama’a.

Karanta wannan: NiMet ta yi hasashen samun jinkirin saukar ruwan sama a bana

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Laraba.

“Shugaban hukumar ya jaddada cewa duk wani jami’in da aka samu da laifin yin amfani da sunansa da laifin zamba ko karbar kudi zai fuskanci hukunci mai tsanani. Daga nan sai ya bukaci jami’an da su tabbatar da gaskiya da sanin ya kamata, yana mai jaddada cewa mutuncin rundunar ‘yan sandan Najeriya na cikin hadari idan ba a duba irin haka ba, inji sanarwar.

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya ta yi barazana da takunkumi kan ma’aikatan Gwamnati

Bugu da kari IGP Kayode Egbetokun ya roki jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani yunkuri na amfani da sunansa wajen yin zamba ko karbar kudi, musamman wajen binciken al’amura.

Ya bayyana irin muhimmiyar rawar da ‘yan kasa ke takawa tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda don kiyaye kyawawan halaye da kuma kawar da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.

Cikin sanarwar, “Jama’a na iya tuntubar ‘yan sandan Najeriya ta kafafen sada zumunta na zamani da lambobin waya 08057000001 ko 0805700002 da 08057000003 da kuma 07056792065.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here