Allah bai kaddara Atiku ya mulki Najeriya ba – Bwala

imgonline com ua twotoone zwGYUuXexuI3l 750x400

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Bola Tinubu kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya kawar da duk wani fatan da zai dade yana yi na zama shugaban Najeriya.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa har sau shida (ko dai ta hanyar fidda gwani ko kuma a matsayin dan takarar jam’iyya), ana kyautata zaton zai sake yin takara a shekarar 2027, matakin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar kasar.

Da yake magana a lokacin da yake hira a gidan Talabijin na TVC a ranar Litinin, Bwala ya ce gazawar Atiku a lokuta da dama a rumfunan zabe na nuni da cewa watakila ba shi ne kaddara na ya jagoranci kasar ba.

Kalamansa “Kamar yadda tsohon shugabana ya fada, idan har na samu damar haduwa da shi ido da ido, abin da zan fada masa shi ne: ‘Mai girma Alhaji Atiku Abubakar, ka yi imani da kaddara, Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya ga dama, kuma ga dukkan alamu, daga gaskiya a doron kasa, wata kila ba nufin Allah ba ka yi mulkin Nijeriya.

Amma idan ya dage cewa yana son ya tsaya takara kuma yana son zama shugaban kasa, kamar yadda muke gani a yanzu haka, karshen siyasarsa ba zai yi dadi kamar yadda yake tunani ba, domin a halin yanzu, daga danginsa na siyasa, ya yi asarar dimbin mutane, watakila kashi sittin zuwa saba’in cikin dari,” in ji Bwala.

Karin karatu: Gwamnan Kano ya jajantawa iyalan mutane 5 da suka mutu a hadarin mota a Kano

Hadin gwiwar Obi da Atiku zai zama “kuskure”

Bwala ya kuma yi tsokaci game da rade-radin da ake ta yi game da yuwuwar kawance tsakanin Atiku da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, inda ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na iya kawo wa Obi bala’i a siyasance.

A baya Obi ya taba zama abokin takarar Atiku a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 kafin ya kaddamar da nasa takarar shugaban kasa a 2023.

Bwala ya kuma yi watsi da kokarin da aka yi a baya-bayan nan na kafa kungiyar hadin gwiwa domin tunkarar zaben 2027, yana mai cewa kungiyar ta riga ta gaza sakamakon tasirin da Shugaba Bola Tinubu ke da shi a fagen siyasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here