Gwamnan Kano ya jajantawa iyalan mutane 5 da suka mutu a hadarin mota a Kano

Abba Kabir Yusuf sad 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa al’ummar karamar hukumar Danbatta sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar a ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, hatsarin ya afku ne a kusa da Shantake mai tazarar kilomita bakwai daga garin Danbatta, a daidai lokacin da wadanda lamarin ya rutsa da su ke dawowa daga Bauchi bayan sun raka wata amarya zuwa gidan aurenta.

Daga cikin wadanda suka rasu har da dangi guda daya, inda Alhaji Surajo kane ya rasa ‘ya’yansa biyu, yayin da kaninsa, Alhaji Salisu Dan Raino ya rasu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa biyar.

A cikin sakon ta’aziyyar sa, Gwamna Yusuf ya bayyana lamarin a matsayin “mummunan rashi da ya jefa bakin ciki a cikin jihar baki daya.

Ya yi addu’o’in Allah ya jikan wadanda suka rasu da kuma al’ummar Danbatta.

Gwamna Yusuf ya kuma baiwa al’ummar jihar tabbacin goyon bayan gwamnatin jihar a wannan lokaci mai wuya, ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya baiwa iyalansu hakurin jure wannan rashi mara misaltuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here