Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2027

Joash Amupitan INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin babban zaben 2027, inda ta bayyana muhimman ranaku na kada kuri’a, zaben fidda gwani na jam’iyyu, yakin neman zabe da rajistar masu kada kuri’a.

Sanarwar ta zo ne yayin da ake nuna damuwa kan jinkirin amincewa da gyaran Dokar Zabe da ke gaban Majalisar Dokoki.

INEC ta bayyana a ranar 4 ga Fabrairu cewa ta kammala tsara jadawalin zaben da sauran ayyuka duk da jinkirin dokar.

Zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya za su gudana ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2027.

Zaben Gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi za su biyo baya makonni biyu bayan haka, ranar Asabar, 6 ga Maris, 2027.

Yakin neman zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya zai fara daga 18 ga Nuwamba, 2026 zuwa 19 ga Fabrairu, 2027.

Yakin neman zaben Gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi zai fara daga 15 ga Disamba, 2026 zuwa 5 ga Maris, 2027, sa’o’i 24 kafin ranar zabe.

Rajistar masu kada kuri’a ta dindindin za ta fara a watan Afrilu, 2026, kuma za ta kare a watan Janairu, 2027 domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin rajista ko sabunta bayanansu.

Jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaben fidda gwani tsakanin 1 ga Yuli zuwa 30 ga Satumba, 2026, sannan su mika sunayen ‘yan takararsu ga hukumar tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoba, 2026.

INEC ta ce, za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe ranar 15 ga Nuwamba, 2026.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here