Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas da suka hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe, sun amince su hada kai da hukumar kula da Almajirai da kula da Ilimin Yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kasa NCAOOSCE ta hanyar samar da ofisoshi a kowace jiha.
Wannan shi ne sakamakon sanarwar da gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya karanta a karshen taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabas da aka gudanar a Damaturu babban birnin jihar Yobe a ranar Alhamis, inda kungiyar ta kuma yi alkawarin tallafa wa daliban makarantun tsangaya da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Kungiyar ta kuma yi tsokaci kan yadda ayyukan ‘yan tada kayar baya ke kara tabarbarewa a yankin tare da yin kira ga rundunar soji da sauran jami’an tsaro da shugabannin al’umma da su sake farfado da dabarunsu na dakile hare-haren ta’addanci a yankin.
Kungiyar ta himmatu wajen tinkarar matsalolin tsaro ta hanyar tunkarar al’amuran da ke faruwa a halin yanzu tare da magance wasu daga cikin ƙudurorin da suka sa a gaba.”
Kungiyar ta yi la’akari da muhimmancin makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya dake Yola tare da kudurae aniyar tallafawa ds fadadata ta hanyar samar da karin masauki, samar da ruwan sha da sauran kayan aiki domin inganta ta da kuma samar da ingantaccen horo.
Karin karatu: NELFund ta musanta zargin karkatar da kudaden lamunin dalibai
A yayin da kungiyar ta yabawa gwamnatin tarayya da sojojin kasar wajen yakar ‘yan kungiyar Boko Haram, kungiyar ta kuma sake jaddada kudirinta na ci gaba da gudanar da al’amuran da suka shafi yankin da kuma gudanar da kwasa-kwasan gama-gari kan al’amuran da suka shafi hadin kan yankin na tsaro, zamantakewa da tattalin arziki.