Asusun ba da lamunin ilimi na Najeriya NELFund ya karyata zargin karkatar da kudaden rancen dalibai.
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Oseyemi Oluwatuyi, daraktan yada labarai na asusun, ya ce wasu rahotannin kafofin yaɗa labarai suna yawo, da ke nuna cewa ta karkatar da kudaden lamunin dalibai.
Oluwatuyi ya ce wadannan zarge-zargen “karya ne, kuma suna illa” ga amincin shirin.
Idan za a iya tunawa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta ce ta fara gudanar da bincike a kan zargin karkatar da kudaden rancen dalibai.
Wani rahoto ya yi ikirarin cewa manyan makarantu 51 ne ke da hannu wajen cirewa da kuma cin gajiyar shirin na NELFund ba bisa ka’ida ba.
ICPC ta ce daga cikin Naira biliyan 100 da gwamnatin tarayya ta fitar na shirin bayar da lamuni na dalibai, Naira biliyan 28.8 ne kawai aka raba wa daliban har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, inda kusan Naira biliyan 71.2 ba a san inda suka yi ba.
Labari mai alaƙa: Lamunin Dalibai: ICPC ta fara binciken ɓatan naira biliyan 71.2 a asusun rance na dalibai
ICPC ta yi nuni da cewa, ta gayyaci manyan masu ruwa da tsaki domin yi musu tambayoyi da suka hada da babban daraktan ofishin kasafin kudi, babban akanta janar na tarayya, da kuma jami’an babban bankin Najeriya.
An kuma gayyaci Akintunde Sawyerr, daraktan gudanarwa na NELFund, don samar da takaddun da suka dace.
ICPC ta ce NELFund ta samu Naira biliyan 203.8 daga ranar 19 ga Maris, 2024, daga ɓangarori da dama.
Wadannan sun hada da kaso daga Kwamitin rabon arzikin kasa (FAAC), Hukumar Yaki da yiwa tattalin srzikin Kasa ta’annati (EFCC), da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund).
Daga cikin wannan adadi, ICPC ta ce an biya Naira biliyan 44.2 ga cibiyoyi 299 da suka ci gajiyar tallafin, wanda ya kunshi dalibai 293,178.
Oluwatuyi ya ce ba a sace wasu kudade a karkashin shirin rancen dalibai ba, wanda a hukumance an kaddamar da shafin neman bashin a shekarar 2024.
Daraktan sadarwar ya ce NELFund na gudanar da tsarin ba da lamuni na kai tsaye don kawar da yuwuwar rashin samun daidaito na kudi.