Lauyoyin APC da dan takar PDP sun musanta karar da aka shigar kan nasarar Adeleke a zaben Osun

APC PDP Logo 750x430

Tawagar Lauyoyin Jam’iyyar APC a Osun da kuma dan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a zaben 15 ga Agusta, Adebayo Adedamola, sun musanta koke-koken da ake cewa an shigar domin kalubalantar nasar Gwamna Ademola Adeleke.

Sun musanta hakan ne bayan an manna kararraki biyu da ake cewa APC da PDP ne suka shigar a allolin sanarwar Kotun sauraron karar zaben Gwamnan Jihar Osun da ke Osogbo a ranar Litinin.

Kara ta farko, mai lamba EPT/OS/GOV/01/2026, dake dauke da sunan Bola Oyebamiji da APC a matsayin wadanda suka shigar, yayin da ake karar Adeleke, Accord da Hukumar Zabe ta Kasa.

Kara ta biyu, mai lamba EPT/OS/GOV/02/2026, na dauke da sunan Adedamola a matsayin wanda ya shigar, yayin da ake karar INEC, Accord da Adeleke.

Sakataren kotun, Pefe Belemore, ya tabbatar da cewa an shigar da kararrakin kalubalantar sakamakon zaben 15 ga Agusta.

Sai dai Lauyoyin APC sun ce ba su ba da umarnin shigar da wata kara kan nasarar Adeleke, yayin da Adedamola ya ce ba shi ba ne, ba kuma lauyansa ba ne suka shigar da karar a kan gwamnan.

Daya daga cikin lauyoyin mai mukamin SAN, Adekunle Adegoke, ya shaida wa jaridar Punch a ranar Litinin cewa lauyoyin sun baiwa Oyebamiji dan takarar jam’iyyar shawara da kada ya kai kara kotu bayan zaben.

Ya ce sun zauna da Oyebamiji da sauran shugabanin jam’iyyar bayan an sanar da sakamako kuma sun yarda cewa kai kara kotu ba zai amfanar da jihar ba.

“Tun daga rana ta biyu bayan zaben, a matakin tawagar lauyoyi da manyan lauyoyi kusan hudu ke jagoranta Dr Biodun Layoonu SAN, Dr Yomi Aliyu SAN, ni kaina Kunle Adegoke SAN da Dr Muritala Abdulrasheed SAN,” in ji Adegoke.

Ya ce lauyoyin sun ba Oyebamiji shawarar cewa abinda ya fi dacewa a wannan yanayi shi ne kada mu je kotu.

A cewar Adegoke, dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki shi ne domin rage tashin hankali da ba wa zaman lafiya dama ya ci gaba da wanzuwa a Osun.

“Ba mu da wani abu na kashin kai tsakaninmu da Nurudeen Adeleke, gwamnan, ko wani daga wata jam’iyya kamar PDP ko Accord,” in ji shi.

Ya ce sun san akwai kwararan dalilai da za su iya amfani da su wajen kalubalantar sakamakon, amma sun yanke shawarar ba da dama mutanen jihar su huta”.

‘OYEBAMIJI YA TAYA ADELEKE MURNAR ZABE BA TARE DA TILASTA BA’

Adegoke ya ce shawarar Oyebamiji na taya Adeleke murnar zabe ta yi daidai da shawarar da tawagar lauyoyin ta ba shi.

“Tun daga ranar 16 ga Agusta da aka sanar da sakamakon zaben, shi ya sa muka ba da lokaci kadan kafin wanda muke wakilta ya fito ya taya Gwamna Nurudeen Ademola Adeleke murna,” in ji shi.

Ya yi tambaya, yaya zai yiwu Oyebamiji ya ba da umarnin shigar da kara bayan da ya taya Adeleke murna da kansa?

“Wanda muke wakilta, bayan ya taya Gwamna Adeleke murna da yardarsa, ba tare da an tilasta masa ba, za ku yi tunanin mutum mai daraja Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji ya je ya ba da umarnin shigar da kara a boye?” in ji Adegoke.

Ya bayyana karar da aka manna a kotun a matsayin takarda da wasu mutane dake nuna kamar lauyoyin APC suka shigar.

“Ina so na bayyana cewa tawagar lauyoyin APC ta musanta wannan takarda da wasu mutane suka shigar. Ba APC ce a matsayin jam’iyya ko dan takararta ya ba da umarni ba,” in ji shi.

DAN TAKARAR PDP YA MUSANTA SHIGAR DA KARA

Dan takarar gwamna na PDP, Adedamola, ma ya musanta bayar da umarni ko shigar da karar kalubalantar nasarar Adeleke.

A cikin hirar da ya yi da TVC a ranar Litinin, Adedamola ya ce lauyansa ko wani shugaban PDP bai taba sanar da shi matakin kalubalantar zaben ba.

“Babu wata kara da ni ko lauyana muka shigar. Don haka ban san inda suka kirkiro wannan karar da suka kai kotun ba,” in ji shi.

Adedamola ya ce babu dalilin da zai sa ya kalubalanci Adeleke saboda ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan a fili kafin zaben kuma ya kada kuri’ar sa.

Ya bayyana cewa PDP ta yi taron manema labarai a ranar 13 ga Agusta inda suka bayyana goyon bayansu ga Adeleke.

“Ba a taba yin wani taro da aka yanke shawarar kalubalantar nasarar a kotun ba,” in ji shi.

“Bayan na kada kuri’a ga Gwamna Adeleke na jam’iyyar Accord. Don me zan canza yanzu in je in shigar da kara a kan sa.”

An ayyana Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamna na 15 ga Agusta bayan ya samu kuri’u 511,067.

TheCable

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here