Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ja kunnen masu yaɗa manufofin neman ƙara nema masa wa’adi da su ƙaurace wa haka kasancewar ba shi da sha’awar ƙarin wa’adin mulki kwata-kwata.
Hakan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mashawarcinsa a fannin yaɗa labarai Malam Garba shehu wadda aka rabawa manema labarai.
Haka kuma sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin ganawarsa da wasu ƴan Najeriya mazauna ƙasa mai tsarki lokacin da yake shirin dawowa gida bayan kammala taro da kuma aikin Umara.
Sanarwar ta ruwaito shugaban na cewa, “Na rantse da Alkur’ani iyakacin wa’adin mulkina zan yi karo biyu kamar yadda kuma kundin tsarin mulki ya tanadar kuma da zarar lokaci ya yi tafiya zan yi, babu batun tazarce, don haka banason wani mutum ya nema mun ƙarin wa’adi”
“Kunga lokacin da aka ce na faɗi zaɓe a karo na 3, cewa na yi Allah na nan, hakan ya sa abokan hamayya ke ta yi mun dariya, amma da Allah ya karbi addu’ata yau me gari waya?” inji shi.
“Kuma gaskiya babban abinda ke ci mun tuwo a ƙwarya a yankunan Arewa maso yammacin Najeriya shi ne zubda jini tare da sace-sacen da ke yawan faruwa, hakan na tada mun hankali, kan haka zan yi iyakar iyawa ta domin ganin an yiwa tufkar hanci.
A jawabansu jakadan Najeriya a birnin makkah Yahaya Lawan da takwaransa na birnin jedda Abdulkarim Mansir sun tabbatar da cewa akwai yan najeriya kimanin Milyan 2 da ke rayuwa a kasar ta Saudi Arabia.













































