Gwamnatin Kano sha alwashin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta

Murtala Sule Garo sabo
Murtala Sule Garo sabo

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada ƙudirinta na bada fifiko a ɓangaren ilimi domin magance matsalolin yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar Kano.

Kwamishinan ƙananan hukumomin jihar Alhaji Murtala Sule Garo ne ya yi wannan alwashin yayin da yake raba kayan karatu ga kananan hukumomin Kano 44.

Alhaji Murtala Garo wanda ya samu wakilcin shugaban shugabannin ƙananan hukumomin Kano watau ALGON Alhaji Muhammad Baffa Takai shugaban ƙaramar Takai ya ce, an shirya shigo da tsarin wanda na gwamnatin jihar Kano ne domin tallafa wa ɓangaren ilimi.

Alhaji Baffa Takai ya kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa kashe maƙudan kuɗaɗe don sayen kayayyakin da za su taimaka wajen inganta fannin ilimi a jihar.

Hakan na cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar ƙananan hukumomi Faruk Ghali Masanawa.

Sanarwar ta ce, kwamishinan ya bada tabbacin cewa gwamnatin za ta cigaba da tallafa wa ilimi ga ilahirin makarantun Firamare da Sakandire kamar yadda ta ke yi a kowanne wata.

“A tsokacin da ya yi a madadin ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomi Alhaji Mannir Dahiru Maigari wanda shi ne shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado ya yi alƙawarin bibiyar yadda rabon kayayyakin zai kasance don tabbatar da ingancin yadda rabon kayan zai kasance a kowacce ƙaramar hukuma”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here