Kano: An samu shugabanni 4 da ke iƙrarin lashe zaɓen shugabancin jam’iyyar PRP

PRP logo gold
PRP logo gold

Rahotonni sun tabbatar da cewa an samu mabanbantan shugabanni 4 a zaɓukan shugabannin Jam’iyar PRP da aka gudanar a ƙarshen mako a Kano.

Jaridar solacebase ta lura cewa an gabatar da zabukan ne a wurare daban-daban da ya kai ga haifar da samun shugabanni guda 4 a jihar waɗanda kowannen su ke iƙrarin lashe zaɓen.

Waɗanda ke iɗrarin lashe zaɓen Shugabancin na PRP  akano sun haɗar da Alhaji Sammani Sharu da Abdulmajid Tarauni da Muntari Zango da kuma Abba Sule Na Matazu, la’akari da takaddamar da ke faruwa tsakanin tsohon jagoran jam’iyyar da wasu shugabanninta a jihar.

Alhaji Abba Sule Na Matazu shi ne wanda aka zaɓa bisa masalaha a matsayin shugaban Jam’iyar a gidan Mumbayya, ya yi alkawarin tafiya da kowa domin farfaɗo da ruhin Jam’iyar a jihar.

Kwamitin mutane 7 ne suka gudanar da zaɓen shugabannin a gidan Mumbayya bisa jagorancin Ibrahim Sulaiman wanda kuma ya samu sahalewar hukumar zaɓe ta ƙasa.

Sabon shugaban PRP Alhaji Na Matazu ya ce, taron Jam’iyyar ya sake fidda ƙarin mambobi 16 da aka zaɓa bisa masalaha don jagorantar kwamitin gudanarwa na jiha.

Da yake yiwa jaridar Solacebase ƙarin haske, sakataren gudanarwar jam’iyyar na ƙasa Alhaji Ibrahim Sulaiman ya ce, Jam’iyyar a matakinta na ƙasa ta amince ne kawai ga taron shugabannin da aka gudanar a gidan Mumbayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here