Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta amince kuma ta wallafa sunan Godswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC mai wakiltar Akwai Ibom ta Arewa/Yamma a zaben 2023.
Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, ya ce INEC ta saɓa doka da ta ƙi karbar sunan Akpabio ta kuma wallafa duk da cewa jam’iyyar APC ta aika da sunan a matsayin dan takararta.
Dakaci karin bayani……













































