Yanzu Yanzu: Farfesa Shehu Dalhatu ya rasu

Shehu Dalhatu
Shehu Dalhatu

Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu rasuwa, babban malami a tsangayar kimiyyar siyasa da ke Jami’ar Bayero ta Kano.

Majiyar jarida Solacebase daga iyalan mamacin ta ruwaito cewa, marigayin ya rasu a daren Juma’a awani asibitin ƙasar Masar sakamakon rashin lafiya.

Sanarwar ta ce an kammala dukkan shirye-shirye domin dawo da gawar sa domin yi mata sutura.

Farfesa Dalhatu ya yi digirinsa na farko da na biyu a sashien mulki da gudanarwa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 1984, yayin da ya dora digirinsa na uku a tsangayar kimiyyar siyasa.

Kafin rasuwar sa, Farfesa Dalhatu shi ne babban daraktan cibiyar bincike da tabbatar da dimukradiyya ta Aminu Kano dake gidan mumbayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here