Wani babban malami a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi, ya sanar da rasuwar mahaifinsa.
Kurfi ya sanar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa mahaifinsa ya rasu a daren ranar Alhamis.
Karin karatu: Tsohon alkalin babbar kotun jihar Kano mai shari’a Wada Rano ya rasu
Tsohon shugaban sashen sadarwa na Jami’ar ya kuma bayyana cewa an yi Sallar Jana’izarsa ne da safiyar Juma’a a garin Kurfi da ke Jihar Katsina.
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, cikin damuwa na ke ba da labarin cewa mahaifina ya rasu a daren ranar Alhamis,” Yana mai addu’ar Allah ya jikansa da gafara.













































