Jami’an lafiya sun gano wani mutum da aka garkame cikin daki tsawon shekaru 20

IMG 20221012 WA0295
IMG 20221012 WA0295

‘Yan sanda a ranar laraba ne suka yi nasarar ceto wani dattijo mai shekaru 67 da aka kulle a daki sama da shekaru 20 a Kaduna.

An gano mutumin ne tsirara kulle awani daki dake wani gida dake kan hanyar Bayajidda a cikin garin Kaduna.

Mazauna ginin sun tsere adaidai lokacin da tawagar ‘yan sanda sukaiwa gidan tsinke.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jalige ya ce wasu jami’an kiwon lafiya na muhalli da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa ne suka fara gano matumin mai suna Ibrahim Ado wanda ke cikin gidan a kulle.

A cewar wani shedar gani da ido, jami’an kula da muhalli sun ziyarci gidan a yau domin duba wasu abubuwan sha da aka ajiye a gidan, inda ba zato suka gano wani mutum a kulle cikin daki.

A cewar majiyar, sun kulle shi kusan shekaru ashirin kenan.

“Komai da komai nasa a dakin yake yi”.

“Sun kai rahoto ga Magajin Gari, kuma kwamishinan ‘yan sandan ya umurci jami’ai da su cafke wadanda abin ya shafa.

“Ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don bayyana gaskiyar al’amuran da kuma dalilin da ya sa aka kulle shi na tsawon wannan lokaci,” in ji shi.

Jalige ya ce tuni aka garzaya da wanda abin ya shafa asibiti domin dubawa dakuma tantance lafiyar sa.

Jalige ya ce an kai wanda aka kashen asibiti domin a tantance lafiyarsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here