Majalisar Dattawa ta kammala tantance mutane uku da shugaba Bola Tinubu ya tura mata sunan su domin a tabbatar da su a matsayin jakadu, waɗanda suka fito daga jihohin Ogun, Jigawa da Oyo.
Tantancewar ta gudana ne a gaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar dattawa ƙarƙashin jagorancin Sanata Sani Bello na yankin Niger ta Arewa.
Masu neman mukaman sune Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa, da Ayodele Oke daga jihar Oyo, kuma sun bayyana gaban kwamitin domin amsa tambayoyin da suka shafi cancantarsu.
Kwamitin ne ya gudanar da tantancewa a madadin majalisar dattawa, inda ya duba tarihin aiki da nagartar kowane ɗaya daga cikin su.
Ana sa ran rahoton kwamitin zai isa zauren majalisar domin tattaunawa da kuma yuwuwar tabbatar da sunayen a mataki na gaba.
Wannan mataki na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya aike da wasiƙa ga majalisar makon da ya gabata domin neman a tabbatar da su.
A yayin zaman tantancewar, kwamitin ya tabbatar da cewa Ayodele Oke ya wanke kansa daga duk wata tuhuma da aka taɓa danganta da shi a baya, lamarin da ya buɗe masa hanya cikin tsari.
Wannan ya biyo bayan nazarin bayanai da kwamitin ya yi kafin tantancewar ta yau.













































