Ƴan sanda sun cafke ɗan shekara 18 bisa zargin kashe abokinsa a Kano

police 1 750x430 1
police 1 750x430 1

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kanio ta cafke wani matashi ɗan shekara 18, Saminu Bala, bisa zargin kisan abokinsa a Kofar Mazugal a birnin Kano.

Daily Trust ta rawaito cewa Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kisan cewa cacar-baki ce ta ɓarke tsakanin Bala da marigayi Ibrahim Khalil sai shi Bala ɗin ya daki Khalil, lamarin da ya janyo mutuwar sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here